Yadda darussan gidan radiyo ke taimaka wa Bintu wajen cigaba da koyon karatu a lokacin nan na annobar COVID-19

Marielle Issa  | 

(Hoto daga Ace Charity)

(Hoto daga Ace Charity)

Bintu mai shekaru 11 ta faɗi yadda ACE Radio School ta ba ta damar cigaba da koyon karatu a lokacin da aka tare kowa a gida aka hana fita.

Bintu, daliba ce ‘yar Nijeriya mai shekaru 11 daga jihar Borno. Ajin shida na firamare wani lokaci ne mawuyaci a matakin shekarun karatu kuma mai muhimmanci. A daidai lokacin da take shirye-shiryen rubuta jarabawa na ƙarshen zangonta a firamari, wanda shi zai ba ta dama ta cigaba da karatunta zuwa makarantar sakandare.

Amma a watan Maris na shekarar 2020, annobar cutar ta COVID-19 ta shigo Nijeriya wanda aka sanya dokar kulle na zama a gida a ƙasar baki ɗaya a wannan lokaci. An rufe makarantu a duk faɗin kasar - gami da na Bintu, a kokarin daƙile yaɗuwar cutar. "Kullen bai yi min daɗi ba saboda ban sami damar zuwa makaranta ba," in ji Bintu. Bani da hanyar amfani da kwamfuta ko yanar-gizo wato intanet, haka nan Bintu ba ta sanu damar zuwa wani waje na nesa don cigaba da karatun jarabawarta ba.

Malala Fund Education Champion Kiki James. (Hoto daga Kiki James)

Malala Fund Education Champion Kiki James. (Hoto daga Kiki James)

Rashin samun hanyoyin karatu na kimiyya da fasaha babbar matsala ce ga karatun 'ya’ya mata a faɗin Najeriya, wanda cutar ta COVID-19 ya katsewa karatunsu na tsawon lokaci mara misaltuwa. Sai dai gwamnatin Najeriya ta samar da hanyoyin karantarwa ga na nesa ta hanyar yanar-gizo wato intanet, da na’urar Talabijan da ma na radiyo. A binciken da ƙungiyar tallafawa ta Malala Fund suka gabatar, sun nuna kashi 10% ne kawai na ‘yan mata a jihar Kaduna ke samun waɗannan hanyoyin karatun. Bugu da ƙari, a cikin iyalai 1,300, bincike ya nuna tara ne kawai daga cikin suke samun karatu ta hanyar kimiyya da fasaha daga makarantu ko wani sashe na hukumar ilimi.

Yayin da Bintu ke zaman gida lokaci da aka rufe makarantu, a wannan lokaci ne Bintu ta fara sauraron radiyo tare da Mahaifinta. Wata rana da yamma, ta ji sanarwa a kan ACE Radio School za ta fara watsa shirye-shiryenta a jihar Borno – nan taƙe ta tsume da farin ciki. Wanda wannan shiri na ACE Radio School kuwa Kiki James ce ta assasa shi, a ƙarƙashin hukumar ‘Malala Fund Education Champion’ don ilimantarwa ga ɗalibai da ke yankuna masu nisa a Najeriya da ba su samun damar amfani da yanar-gizo. A lokacin wannan annobar, ana gudana da shirye-shiryen ne cikin kwanaki uku a kowane mako a jihohi tara domin ɗalibai kamar Bintu su cigaba da samun ilimi a yayin da suke kulle a gida don kariya daga kamuwa da cutar, sun samu ilimi a darussa a fannonin ilimi kamar a fannin Literacy, Numeracy, da kuma Science wato kimiyya.

Ba don ACE Radio School ba, da na manta abubuwa da yawa da na koya a baya. Tun lokacin da na fara sauraron shirin ACE Radio School, na koyi sautukan haruffan Turanci (wato letter sounds) da kuma lissafi, sannan kuma na san kalmar Benevolent (wato kyautatawa).
— Bintu

A Kowace ranar Litinin, Bintu takan ari radiyon Mahaifinta don ta saurari shirin ACE Radio School tare kuma da ƙawayenta da ‘yan’uwanta. "Ba don ACE Radio School ba, da na manta abubuwa da yawa da na koya a baya,” in ji Bintu. Haka nan ta cigaba da ce wa “Tun lokacin da na fara sauraron shirin ACE Radio School, na koyi sautukan haruffan Turanci (wato letter sounds) da kuma lissafi, sannan kuma na san kalmar Benevolent (wato kyautatawa).” Ga Bintu, waɗannan darussan da ake gabatarwa a radiyo, dama ce na samu na koyon sabbin abubuwa a yayin da aka rufe makarantarta, haka kuma hutu ne daga takurin rayuwar kulle. "Ina son Malama Rukky saboda tana koyar da darasin science wato kimiyya, wanda shi ne fannin ilimi da na fi so, kuma tana koyarwa da kuzar.” Haka nan Bintu ta ce. "Ina kuma son Mrs. E. saboda a lokacin da take karantar da sautuka, ta kan rera mana waƙoƙi."

A Najeriya, samar da hanyar karantarwa wanda ba sai a makaranta ba zai ba wa ‘yan mata kamar Bintu damar cigaba da karatu ko da kuwa ba zaman lafiya a ƙasar ko a yayin rikici. "Yana da muhimmanci a ci gaba da karatu ko da kuwa makarantu a rufe suke,” in ji Bintu, wacce ta ci jarabawarta ta shiga makarantar sakandare wato common entrance, wanda ya ƙara mata kuzari a wajen cimma burinta a rayuwarta nan gaba. "Ina so in zama likita kuma in taimaka wajen ceto rayuka." Ko da kuwa an buɗe makarantu a Najeriya, tabbas Bintu a shirye take.

flower.png
Meet the Author
Meet the Author
Marielle Issa

(she/her) is a former editorial associate at Malala Fund. She loves cold weather, chocolate croissants and the novel “Little Women.”