Yadda za a magance matsalar yanayi ta mahangar – mata matasa
Yara mata daga Bangladesh, Honduras, Nigeria, Samoa da sauransue sun bada ra'ayoyinsu akan dokokin yanayi.
Mata matasa sune a sahun gaba a fannin fafutika a bangaren yanayi Daga shirya yajin aiki da rubuta abubuwan da dumamar yanayi ke jawowa zuwa fafutika domin a kara ilimin yanayi a cikin kundin koyarwa na makarantu, suke jagorantar yunkurin samun makoma mai kyau mai ɗorewa.
Matsalolin yanayi yana shafar yara da manyan mata sosai. Matsanancin yanayi da ƙarin zafi ke haifarwa — kamar fari, ambaliyar ruwa da ruwan sama mai nauyi — yafi kashe mata akan maza kuma yafi kashe mata matasa. kuma kaso 80% na mutanen da suka rasa matsugunnansu saboda sauyin yanayi mata ne.
Duba ga wannan banbancin, yana da muhimmanci cewa muryoyin manya da yara mata su taka rawa a yunkurin samo mafita. A ranar mata ta duniya, zamu haskaka rawar da mata matasa ke takawa a fafutikar yanayi da ra'ayoyinsu na kare duniya. Ƴan gwagwarmaya takwas ne suka fada mana abubuwan da suke so shuwagabannin al’ummarsu su yi domin magance matsalolin yanayi — kuma tare dataimakon mai fasahar zane-zane Andrea Pippins — muka raya ra'ayoyinsu ta hotuna.
“Akwai buƙatar sauyi game da yadda muke tunani akan ma'adanai a Honduras, gujewa dagaamfani da su domin riba zuwa fifita killacewa. Cire bishiyoyi yana kan raba dabbobi da gidajensu, kuma yana haifar da janyewar koguna. Ya kamata gwamnati ta kara kokartawa ta fannin shiryawa da daukan nauyin kokarinta akan yanayi. Bugu da kari, kamfanoni da yawa na maida hankali ne kawai akan damuwarsu, ba tare da an hukuntasu akan illar da suke wa ma'adanan mu ba. Wasu makasa masu alaka da wani kamfanin tara ruwan dam sun kashe 'yar gwagarmaya ta gida Berta Cáceres saboda ta yi magana akan gina sabuwar ma'ajiyar ruwa ta dam da illolin da zai yi wa al’ummarta. Bai kamata abar haka ya faru ba. Ina fatan watarana shugabanninmu za su fahimci fa'idar ƙasarmu da kuma cewa ba za mu iya ci gaba da lalata ma'adananmu saboda ribar kuɗi ba.”
— Genesis Lanza, Honduras
"Matakin da muke so shugabanninmu na arewacin Najeriya su ɗauka shi ne su maida karatun yanayi tilas a makarantu, tun daga matakan farko. A bawa matasa dama su yi ilimi domin fadan ra'ayinsu akan yadda za su iya bada gudunmawa mai yawa domin dakile matukar hatsarin sauyin yanayi a cikin al’ummar su. Ba za'a ƙyale shugabanni ba su kaɗai suna ɗaukar matakai akan hanyoyin samun mafita; ya kamata a bada guri a teburin damarmaki ga matasa da manya na yin ƙirkira ta fasaha. Kuma ina so na ga daidaito wajen wakilcin manya da yara mata a cikin hidimar daya shafi yanayi. Canjin yanayi yafi shafan yara da manyan mata kuma ya kamata aji muryoyinsu yayin yanke hukuncin yadda za a dauki mataki."
— Hannatu, Najeriya
“Ina fatan shuwagabannin al’ummata za su kawo karshen damar da kamfanoni da masana'antu ke da shi na sayen ladan rage gurɓata yanayi, saboda idan har zamu samu wani ci gaba akan matsalar sauyin yanayi sai mun rage watsuwar gurbatacciyar iska matuka a maimakon bawa kamfanoni daman watsa iskar gas mai gurbata yanayi. Idan wasu kamfanoni za su iya samun riba ba tare da fitar da gurbatacciyar iska mai yawa ba to saura ma za su iya. Ina kuma fatan za su fifita amfani da makamashi mai sabuntuwa kamar na hasken rana, mai samar da lantarki daga ruwa da iska a masana'ance kuma a yunkurin ƙarfafa wannan ƙoƙarin, a maida makamashi mai sabuntuwa ya kasance mai arawa da saukin samu gurin kamfanoni da sauran jama’a.”
— Kirthana Sivabalan, Maleshiya
“Zan so shugabanninmu su ƙara ilimin sauyin yanayi a cikin tsarin karatu saboda ɗalibai su samu damar sanin illar shi da matakan magance su. Dalibai za su iya koyon kashe wutar na'ura mai kwakwalwa a ajujuwa da dakunan taro in ba kowa, ƙara sarrafa robobi da tafiya ko hawan keke yayin zuwa ko dawowa daga makaranta. Ina fatan shugabanninmu za su samar da ayyukan gyara yanayi. A misali, saƙa kwandon shara masu ban sha'awa ta hanyar amfani da robobin da ka sake sarrafawa, wanda hakan zai magance mafi girman abunda ke gurbata tekunan duniya kuma ya samar da ayyukan yi.”
— Evelyn Acham, Uganda
“Ya kamata shugabannin al’umomi su sa hannun jari a masana'antun tace gishiri daga ruwa, wanda ke cire gishiri daga ruwan gishiri domin samar da ruwan sha mai tsafta wa mutane. A fadin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), mutane miliyan 785 ne a duniya ba su da damar samun ruwan sha mai tsafta, wanda hakan yana shafan dabbobi da tsirrai. Sauyin yanayi yana iya zafafa da kara yawan faruwa fari. Shugabanni za su iya gyara wannan matsalar ta hanyar sanya hannun jari a masana'antun tace ruwa, wanda za'a gudanar dasu damakamashi mai tsafta.”
— Farah Mkaouar, Tunisia
“Ina son naga shugabanni sun ilimantar da yara mata kan haihuwa da ƙarin yawan mutane a makarantu ta yadda yara mata za su samu ilimin iya daukar mataki na ƙayyade iyali. Idan ɗalibai suka koyi wannan a shekarun balaga, zai rage nauyin dake kan ma'adanan da ake da su da kuma matsalar sauyin yanayi. Kuma ina so shugabanni su tabbatar da yara mata suna samun damar yawon buɗe ido daya shafi yanayi, wanda ke faruwa yayin da matafiyi ya zauna da mutanen gari, ya taimaka wa tattalin arzikin garinba tare da takurawa halittun da suke zama wajen ba.”
— Shamma Islam, Bangladesh
“Zan so shuwagabannin al’ummomin duniya su kula da matsalar sauyin yanayi kamar iyalansu ne a sahun gaba wajen fuskantar matsalar. Su ji bukatardaukar matakin gaggawa akan matsalar yanayi da tashin teku. Zan so shuwagabannin al’ummomin duniya su fuskanci matsalar sauyin yanayi yadda lamarin yake, kar-ta-kwana ga dukkan mutanen duniya. Zan so a ƙarshe su sanya mutane sama daiko ko riba. Zan so shugabanni su fita a hankali daga zamanin man fetur su kuma tabbatar da sauyi zuwa amfani da makamashi mai sabuntuwa, inda bukatar ma’aikata ake sanya ta sama da na masana’antu.”
— Brianna Fruean, Samoa
“Zan so shuwagabanni su saurari matasan su. Na yi imani cewa matasan ‘yan asali, musanman ma su, sun fuskanci lamura a rayuwarsu, wanda ya sanya su rayuwa daban da na waje. Suna daukeda ilimi wanda ya sha bam-bam da duk wani tsatstsauran tsari. Daga mahanga ta, hakan shine mafita mafi dacewa. Kuma dama al’umma ‘yan asalisune a sahun gaba wajen fuskantar matsalar sauyin yanayin. A don haka ne idan har muna son mu gyara matsalar, idan da gaske muna so mu fuskanci ainihin sakamakon matsalolin sauyin yanayi, mutane ‘yan asaliya kamata muna dubawa.”
— Tokata Iron Eyes, Amurka
Wasu matakai ne kuke son gani daga shuwagannin ku? Ku bada ra'ayoyinku wajen gyara matsalar sauyin yanayi a nan.