Lalacewar Tsarin Jami'a Najeriya

Aladeselu Margaret Ayomikun  | 

(Courtesy of Aladeselu Margaret Ayomikun)

(Courtesy of Aladeselu Margaret Ayomikun)

Aladesulu Margeret Ayomikun mai shekaru sha takwas 18 da haihuwa ya rubuta akan matsalolin da 'daliban jami'a suke fuskanta a Najeriya.

Na yarda da cewa kowa yanada hakkin samun Ingataccen ilimin Jami'a — ammma hakan yayi daban da abunda kefaruwa a ƙasar Najeriya. Akwai yardaddun Jamio'i Ɗari da saba'in 170 a Nigeria. Cikinsu guda arba'in da uku ne 43 mallakin gwamnatin tarayya, guda arba'in da takwas 48 mallakin Jahohi, da kuma guda saba'in da tara 79 masu zaman kansu. A duk daka haka, ƙasar Najeriya tanada yawan mutane da suka kai miliyan ɗari da tamanin 180m, wanda kashi sittin da biyu cikin ɗari 62% matasane masu shekaru ashirin da huɗu 24 zuwa ƙasa. A takaice babu jamio'i da zasu wadaci yawan daliba Najeriya. Bincike yanuna, a takaice dalibi ɗaya ne acikin kowani dalibai huɗu da suka nemi shiga jami'a suke samun gurbi: kaso mafi yawa basu samun shiga jami'ar bawai domin basu cika ka'idojin shiga ba saidai don babu wadataccen gurbi a jami'ar.

Koda dalibi yasamu shiga jami'a, to babu tabbacin cewa zai samu ingattaccen ilimi. Jamio'inmu basuda gini dakuma wajajen horo na ilimi da ake buƙata domin karfafawa dalibai gwiwa. Kamarsu wadatattun dakunan koyarda karatu, Dakunann dalibai wadatattu kuma masu faɗi, Wajajen cin abincin dalibai, Malaimai masu zuciyar koyarwa, taimako na fannin kuɗi, dakunan ajiyar littafi domin karatun dalibai cikin nutsuwa, Ingataccen asibitin dalibai da sauransu. Tun Kafin fara sabon zangon karatu, malamai kan iya nuna daliban da zasuyi nasara a jarabawar zangon. Akan maimaita aji saboda rashin nasara a darasi ɗaya kacal. Kuma akan samu mafi girman sakamon jarabawa ba tareda an koyi komai ba.

Abun yakanfi haka muni wajan daliba mace, domin sukan kasance cikin addu’a kullum domin kar malami ya nemi saduwa dasu a domin samun nasarar jarabawa.
— Aladeselu Margaret Ayomikun

Abun yakanfi haka muni wajan daliba mace, domin sukan kasance cikin addu'a kullum domin kar malami ya nemi saduwa dasu a domin samun nasarar jarabawa. Yazama tilas akan dalibai mata su saurari abinda mai karantarwa namiji keso a fannin sutura da zasu saka, maganan da zasu faɗa musu in sun tambayesu, cikin taka tsan-tsan saboda jamio'in Najeriya suna cike tam da munanan labaru na muzanci a kan jinsin mata. Nakan yi tunanin jarabawa cikin firgici da tsoro ba domin bazan iya amsa jarabawarba, sai don mai karantarwa zai iya hanani shiga rubutawa saboda nasanya zobe a hanci ko kuma ado da tsawon faratuna. 

Wannan shekarar, daliban makarantun gwamnati sun fuskanci mafi tsanantan matsala, saboda yajin aiki mai tsawo da kungiyar malamai na jamio'i (ASUU) sukayi, saboda rashin kula da jami'a ta fannin kuɗaɗe da kuma tsarin biyan albashin masu karantarwar. Sakamakon rashin tausasawa na gwamnatai makarantu ke kulle tun watan Maris na shekarar 2020 wanda a takaice yakai watannin goma 10. Hakan yana nufin wata na goma ban shiga aji domin koyon karatu ba. Duk da cewa an samu sasantawa a watan Dizamba 2020, dalibai suna cikin tsoron cewa za'a iya komawa yajin aikin bada jimawa ba.

(Courtesy of Aladeselu Margaret Ayomikun)

(Courtesy of Aladeselu Margaret Ayomikun)

A cikin watanni goma na farko cikin yajin aikin, komai ya tsaya cak a fannin ilimin daliban jamio'i mallakar gwamnati, wanda hakan a takaice yana nufin babu wani shiri na komawarmu makaranta don cigaba da karatun mu. A yayin da mu daliban jamio'in gwamnati ke gida, 'yan uwanmu dalibai na makarantu masu zaman kansu basu san menene wani tsayawar karatu ba. Domin suna karatunsu, suna jarabawa, suna canza zangon karatu (A yanzu haka sa'anninmu sun wucemu da shekara a makarantar kuɗi).

Saboda tsoron irin wadannan matsaloli dayawar mutane ke tsoron ficewar dalibai masu yawa daga makaranta. Matasalar da hakan zai janyo wa lafiyar tunanin wadannan dalibai yanada matuƙar yawa. A ƙashin kaina, watanni goma da suka wuce na samu matsalar matsanancin tsoro da mugun tunani. Abun yanada ciwo mutum yasan ƙasar shi bata damu da cigaban rayuwarsa ba, kuma cewa, bazai iya cika burin da yayi wa rayuwarsa ba. Kamar dayawa daga cikin abokan karatuna, na shiga makarantar koyan sana'ar hannu yadda na koyi yadda ake dinkin kaya, don hakan yafi kamada yadda yadace in tafiyarda lokacina. Bayan koyan sana'ar hannu, kammala karatu a lokacin da aka tsara zai kasance mafi kyau.

Gwamnatin Najeriya bata fahimci gwagwarmayar da dalibin jami'ar Najeriya ke yiba, sabodayawanci iyalan masu ruwa da tsaki a gwamnatin sukan tafi wasu ƙasashene domin karatun su na jami'a. Abun takaicine cewa wadanda suke da hakkin gina tsarin ilimi mai inganci sune mutanen da suke da karanci ilimi akan tsarin ilimin.

flower.png
Meet the Author
Meet the Author
Aladeselu Margaret Ayomikun

is an 20-year-old student who spends most of her time writing, singing, listening to her culturally diverse playlist and sketching. She admires the works of Chimamanda Ngozi Adichie and Funmilayo Ransome-Kuti and hopes to be like them. She is passionate about feminism, education and climate change. You can follow her on Instagram and Twitter.