‘Yan uwa mata Muna gabatar muku da mata matasa masu nazarin tsarin shari’a mai adalci da yadda ta shafi 'yancinsu

Hannah W. Orenstein  | 

(Courtesy of Sandra Egboro)

(Courtesy of Sandra Egboro)

Har zuwa shekarar 2016 dokar kasar Zimbabuwe ta ba 'yan mata wadanda shekarunsu na haihuwa suka kai 16 yin aure bisa doka, amma ga yara maza, sai sun kai shekarun18 . Wannan banbancin na shekaru biyu ya yi tasiri sosai a rayuwar 'yan matan Zimbabwe. Kusan kashi daya cikin uku sun yi aure a lokacin da suka kai shekara 18 , mafi yawansu kuwa sun bar makaranta. Hakan ya kasance har Loveness Mudzuru, ‘yar shekara 20, da Ruvimbo Tsopodzi,’yar shekaru 19, suka kai kokensu zuwa ga kotun tsarin mulki ta Zimbabwe. Matan biyu, wadanda suka yi aure suna da shekaru 16, sun ce Dokar Aure ta Zimbabwe ta nuna wariya ce saboda shekarun aure da aka yi sun banbanta da jinsi. A hukuncin da kotun,ta yanke wanda ‘yan matan sukayi nasara ta canza doka ta yadda wani mutum ba zai iya yin aure ba kafin shekara 18. 

A kowace rana kuma a kowace ƙasa, kotuna suna yanke shawara waɗanda zasu iya baiwa, ko taƙaita 'yancin' yan mata, kamar shari'ar Loveness da Ruvimbo. Kodayake, lokacin da matasa ke son yin kira ga canji, ana jan hankalinsu ga wasu hanyoyin bayarda shawarwari kamar su jawabai, tattaki, roko ko yin magana a kan zamantakewa a kafofin sada zumunci. Amma, "A yanayin da ya dace, tsarin adalci na iya zama kayan aiki da gaske ga 'yan mata, " in ji Sabrina De Souza, Manajar Advocacy a Asusun Malala.

Sabrina ta kara da cewa, "Akwai wani imani cewa tun suna matasa, saboda ba su kai shekarun yin zabe ba, cewa muryar su ba ta da mahimmanci, wanda da gaske ne ba daidai ba," in ji Sabrina. "Saboda ya tasiransu dasu kuma yana shafan su sosai, haƙiƙa akwai mahimmin matsayi a gare su suyi magana ..." 

(Courtesy of Anna Salvatore)

(Courtesy of Anna Salvatore)

Ko da ba ku yin shiri game da ƙalubalen da yake tattare da tsarin shari'ar ƙasar ku har yanzu yana da mahimmanci ku fahimci yadda tsarin yake. “yana da mahimmaci kwarai da gaske mutum ya san ‘yancinsa a aikace’’ Cewar Anna Salvatore ta makarantar SCOTUS dake Amurka) High School SCOTUS (Supreme Court of the United States).

Anna ta fara yin rubuce rubuce a blog dinta a watan Fabrairu 2018 game da yadda shari’un Kotun Koli ke shafar manyan makarantu. Ta damu da SCOTUS bayan karanta labarin da ke da alaƙa da fassarar wata shari’a ta Kotun Koli, wanda shine lokacin da lauyoyin suka gabatar da batunsu game da batun, kuma alƙalan suka ci gaba da neman ba’asi Da farko, batun da ke cikin shari’ar ya yi kama da rikirkitaccen batu, amma yayin da Anna taci gaba da karantawa, ta fahimci inda batun yasa gaba har yasa ta farin ciki. Ta nemi ƙarin wasu kararrakin don yin nazari sannan ta fara rubutu game da batun. Yanzu sahafin nata na intanet ya zama wata kafa da matasa ke bada gudummawa daga ko'ina cikin ƙasar waɗanda ke bincika nau'ikan kotu da suka shafi batun.

Duk da yake Anna tana son yin rubutu game da dokoki a matsayin abin sha'awa, a Najeriya kuma, Sandra Egboro ta zama wata ƙwararriyar mai taimaka wa mutane su nemi hakkinsu. Tun lokacin tana karama, Sandra tanaso koyaushe taga tana kare da taimakawa ɗan adam - kawai ba ta da tabbaci ta yaya zata fara. Ba ta gan ba har sai da ta kasance ta cika shekara 9 a lokacin da ta fahimci kuma ta gane shari'arta ƙasar ta inda ta samu amsar ta. 

Mahaifin Sandra, likitan dabbobi ne, wanda dole ya fuskanci shari’a a game da wani hadari day a faru a inda yake aiki.. Bayan shekaru uku - "Shekaru uku masu tsawo a rayuwarmu" – a karshe mahaifinta ya sami 'yanci daga gwagwarmayar da yasha a kotu. Sai dai amma abin ba zai taba gushewa daga zukansu ba. 

"Abinda duk ya faru ya haifar mana da tashin hankali," in ji Sandra. "Kasancewar abida ya faru ga mahaifina game da shari’arsa shine ya bani karfin gwiwar taimakawa jama’ar da basu da yadda zasuyi." A yanzu haka, Sandra tana aiki a matsayin Jami'ar harkokin shari'a tare da (LEDAP) , ƙungiyar ba da agaji ce da ke aiki don haɓaka da kare haƙƙin ɗan adam a Najeriya. Asusun Malala ta tallafa wa aikin LEDAP don aiwatar da dokar Ilimi daga tushe, wanda ke ba da tabbacin samun ilimi kyauta a kananan makarantun gaba da firamare. 

Ko ta hanyar yin nazarin doka ko kalubalatar batu a kotu, yara mata kamar Sandra, Anna, Loveness da Ruvimbo sun bada gudunmawa don tabbatar da gwamnatocinmu su ci gaba da kare haƙƙin kananan yara mata. 

flower.png
Meet the Author
Meet the Author
Hannah W. Orenstein

is a former employee of Malala Fund. She loves Los Espookys and Barbra Streisand’s Instagram.